Jam’iyya mai mulki ta APC a Najeriya ta ce ta amince da zaben da aka yiwa Sanata Bukola Saraki a matsayin sabon shugaban Majalisar Dattawan kasar.
A ranar juma’ar da ta gabata, shugaban jam’iyyar, Chief John Odigie-Oyegun ya bayyana hakan yana mai ba da tabbacin cewa sauran sanatoci sun zabi Saraki, kuma jam’iyyar a shirye ta ke ta yi aiki da shi.
A farkon makon da ya gabata aka gudanar da zaben shugabannin majalisar dattawa da ta wakila inda Saraki ya zama shugaban majalisar dattawan yayin da kuma Yakubu Dogara ya zama kakakin majalisar wakilai.
Dukkanin shugabannin biyu ba su jam’iyyar ta APC ta tsayar a matsayin ‘yan takarar ta ba, lamarin da ya sa ta ce ba ta amince da zaben ba, domin an gudanar da zaben ba da sanin bangaren su Sanata Ahmed Lawal ba da Femi Gbajabiamila.
Wannan lamari ya haifar da cece-kuce a majalisar da ma fagen siyasar kasar wanda hakan ya sa banagren Lawal da Gbajabiamila ke cewa za su shigar da kara a kotu domin kalubalantar zaben, wanda suka ce an gudanar yayin da ba sa nan.
Kakafan yada labaran Najeriya sun ruwaito shugaban jam’iyyar Oyegun ya na cewa jam’iyyar ta APC ta sha magance rikice-rikice da ke kunno kai,saboda haka wannan ma ba zai zama wani lamari na daban ba.