Shugaban Najeriya Muhammad Buhari, ya tafi kasar Afrika ta kudu domin halartar taron koli na kasashen Afrika.
Wannna taro ya kasance na farko da Buhari ke halarta a karkashin inuwar kungiyar ta AU wacce ke gudanar da tarona jiko na 25, bayan da ya karbi mulkin kasar a watan jiya.
Babban batu a wannan taro ya kasance batu ne da ya shafi tsaro, wanda Najeriya ke fama da shi a yanzu haka.
Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta Najeriya ta fitar ta ce shugaba Buhari zai gana da shugabannin kasashen Afrika a gefen taron kan batutuwan da suka hadin da kasashen domin yakar kungiyar Boko Haram.
A ranar Talata a ke sa ran Buhari zai dawo Najeriya bayan halartar wannan taro.