Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kubutar Da Direban Da Kwantena Ta Fada Kan Motarsa A Legas


Motar da kwantena ta fada kanta
Motar da kwantena ta fada kanta

An yi nasarar kubutar da direban da ransa sakamakon daukin gaggawa da hadin gwiwar LASTMA da sauran hukumomin bada agajin gaggawa suka kai, ciki harda hukumar kiyaye afkuwar hadura ta tarayyar Najeriya (FRSC) da takwarata ta bada agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA).

Direban wata mota kirar Toyota Camry, ya tsallake rijiya da baya a yankin Mile 2 bayan da wata kwantena mai tsawon kafa 40 makare da kaya ta fada kan motarsa a Mile 2, kan hanyar zuwa Apapa, ta jihar legas a yau Litinin.

Sanarwar da daraktan sashen hulda da jama’a da wayar da kai na hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Legas (LASTMA), Adebayo Taofiq ya fitar tace an yi nasarar kubutar da direban da ransa sakamakon daukin gaggawa da hadin gwiwar LASTMA da sauran hukumomin bada agajin gaggawa suka kai, ciki harda hukumar kiyaye afkuwar hadura ta tarayyar Najeriya (FRSC) da takwarata ta bada agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA).

Taofiq ya kara da cewar ana cigaba da kokarin kawar da kwantenar data fadi, a yayin da jami’an lastma ke cigaba da kula da wurin da hatsarin ya afku domin rage cunkoson ababen hawa da kuma dawo da doka da oda.

Babban manajan lastma, Olalekan Bakare-Oki ya jaddada mahimmancin daure kwantenoni yadda ya dace daga bangaren direbobi da mamallakansu.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG