Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matatar Dangote Ta Rage Farashin Man Fetur


Matatar mai ta Dangote (Hoto: Facebook/Dangote)
Matatar mai ta Dangote (Hoto: Facebook/Dangote)

An zaftare farashin litar man daga Naira 990 zuwa 970 “domin nuna godiya ga al’ummar Najeriya”.

Matatar Dangote ta rage farashin man fetur dinta ga dillalai.

Babban jami’in kasuwanci da yada labaran matatar ta Dangote, Anthony Chiejina, ya sanarda hakan a sanarwar daya fitar a jiya Lahadi.

Yace an zaftare farashin litar man daga Naira 990 zuwa 970 “domin nuna godiya ga al’ummar Najeriya”.

“A yayin da matatar ba zata yi sakaci game da igancin albarkatun man fetur dinmu ba, muna baku tabbaci a kan samar da kayayyakin da basa gurbata muhalli kuma masu dorewa.

“Mun dukufa wajen kara yawan man da muke tacewa domin biyan bukatu har ma da zarta abinda ake bukata a cikin gida; tare da kore duk wata fargaba ta samun karancinsa.”

Wannan shine karon farko da farashin man zai ragu tun bayan fara cefanar da bangaren man fetur din da gwamnatin Najeriya ta yi.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG