Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabbin Hare-Hare Kan Al’ummomin Benuwe Sun Hallaka Mutane 30


Yan bindiga
Yan bindiga

Kauyuka da dama a kananan hukumomin Katsina-Ala da Logo sun fuskanci mamaya a jiya Lahadi zuwa wayewar garin yau Litinin.

Akalla mutane 30 ne suka mutu a yankuna da dama na kananan hukumomin jihar Benuwe guda 2.

Rahotannin kafafen yada labaran yankin sun ce kauyuka da dama a kananan hukumomin Katsina-Ala da Logo sun fuskanci mamaya a jiya Lahadi zuwa wayewar garin yau Litinin.

Al’ummar yankunan sun ce an gano gawawwaki 10 a shiyar Katsian-Ala yayin da aka tsinto wasu 20 a yankin Logo, abinda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa mutane 30.

Shima shugaban karamar hukumar Katsina-Ala, Justine Shaku, ya shaidawa manema labarai a birnin Makurdi cewa mutane da dama sun mutu a yankinsa sannan an lalata dimbin dukiya.

Takwaransa na karamar hukumar Logo, Clement Kav, ya yi zargin cewa maharan sun yi kirarin mallakar yankinsa, inda suka ce kasar Tombo mallakinsu ce.

“Sun farwa majalisar mazabar Tombo tare da hallaka mutane 17 da jikkata wasu 37.

Gwamna ya riga ya aike da karin jami’an tsaro zuwa yankin harma zaman lafiya ya dawo. A halin yanzu ba’a samu rahoton batan mutane ba,” a cewarsa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Catherine Anene, ta tabbatar da afkuwar lamarin, sai dai tace gawawwaki 5 ne aka gano.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG