Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutun Guda Ya Mutu, 14 Sun Kubuta Sakamakon Dakile Yunkurin Satar Mutane A Katsina


Gwmanan jihar Katsina Umar Dikko Radda.
Gwmanan jihar Katsina Umar Dikko Radda.

Marigayin na cikin mutane 2 da ‘yan sanda suka ceto da suka samu raunukan harbin bindiga kuma aka garzaya dasu zuwa asibiti domin samun kulawar gaggawa a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewar wani mutum da aka yi garkuwa da shi domin neman kudin fansa ya mutu yayin da yake samun kulawar likitoci daga raunukan bindigar da ya samu sakamakon harbin ‘yan bindiga a karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina.

Marigayin na cikin mutane 2 da ‘yan sanda suka ceto da suka samu raunukan harbin bindiga kuma aka garzaya dasu zuwa asibiti domin samun kulawar gaggawa a jihar.

Al’amarin ya faru a jiya Lahadi, da misalin 7 da mintuna 55 na yammaci bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne dauke da muggan makamai, suna harbin kan mai uwa da wabi, suka afkawa wasu motocin haya 2 a kauyen Dan’arau dake kan hanyar Magama zuwa Jibiya a karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina, da nufin yin garkuwa da mutanen dake cikinsu.

A sanarwar daya fitar yau Litinin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq, yace tawagar jami’ai karkashin jagorancin baturen ‘yan sandan yankin, sun yi nasarar dakile yunkurin tare da kubutar da mutane 14.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Aliyu Musa, ya shawarci al’ummar gari dake da bayanai akan ayyukan batagari dasu gaggauta kai rahoto ga caji ofis mafi kusa dasu.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG