Bayan kwana uku da iyalan Alhaji Saidu Yahaya Andarai basu ganshi ba sai suka kai kara wurin 'yansanda cewa maigidansu ya bace.
Rahoton iyalan yasa 'yansanda suka shiga bincike. Daga karshe bincikensu ya kaisu gidan yaronsa Bello Ubandawaki dake unguwar Kwannawa a birnin Sokoto inda aka binne gawar mutumin.
DSP Al-Mustapha Sani kakakin rundunar 'yansandan jihar Sokoto yayi bayani ya kuma tabbatar da yadda lamarin ya auku. Yace yaronsa wanda ya yadda dashi Bello Ubandawaki shi ya gayyaci Alhaji Andarai zuwa Sokoto akan cewa akwai wata kaddara da za'a sayar a Kwannawa cikin Sokoto. Shi Bellon shi ne yake saya masa filaye ko gidaje.
Da Alhaji Andarai ya iso gidan Bellon sai wasu mutane guda biyar suka hadu suka yiwa Alhaji Andarai duka kana suka yankashi kamar rago. Bayan hakan suka haka rami cikin gidan Bellon suka binneshi suka kuma dabe da siminti.
Biyo bayan karar da matar Alhaji Andarai ta kawo yasa aka soma bincike aka kuma je gidan Bello Ubandawaki domin shi ne mutum na karshe da ya ga Alhaji Andarai. A gidansa ne 'yansanda suka ga sabon wurin da aka dabe suka tona sai ga gawar Alhaji Andarai.
Kawo yanzu dai an kama mutane shida da suka hada da shi Bello Ubandawakin. 'Yansanda suna cigaba da bincike amma shi Bello Ubandawaki ya tabbatar da cewa su ne suka kashe Alhaji Andarai.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.