A Nijar, gwamnatin kasar tace ba zata yi kasa a guiwa ba wajen gano ‘yan mata 26 da samari 11 da mayakan Boko Haram suka sace, bayan hare haren da suka kai a Ingilewa a yankin Diffa, a ranakun 2-3 ga watan nan.
Kakakin gwamnatin kasar Asmana Mal Isa ne ya bayyana haka, lokacinda ya bayyana a kafofin yada labaran kasar a daren jiya talata, domin bayyana matsayar gwamnatin kan hare haren da ‘yan binidgar suka kai wanda ya halaka akalla mutane 9.
Wannan hari inji kakakin na gwamnati, yazo ne mako daya bayan wani hari da ‘yan bandigar suka kai a gari da ake kira Kablewa, akan wani sansanin ‘Yan gudun hijira.
A lokacin harin ‘yan kunar bakin wake biyu sun halaka, da wasu mutane biyu. Mutum 11 kuma sun jikkata, hudu daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali.
Daga nan gwamnatin ta yi kira ga al’uma su ci gaba da harkokinsu kuma su baiwa jami’an tsaro dukkan hadin kai da suke bukata.
Kakakin na gwamnati ya kuma mika ta’aziyyar gwamnati da jami’anta ga iyalan wadanda hare haren suka rutsa da ‘yan uwansu.
Facebook Forum