Shugabannin kananan hukumomin da aka kora sun hada da Muhammad Muhammad Illo, Hassan Koma, Musa Matashi, Ali Ahmadu, Abbas Yakuba, da Nuhu Haruna.
Ana kyautata zaton korar tasu tana da nasaba da almundahana da dukiyar kasa kamar yadda shugaban kasar ya taba yiwa shugabannin hukumomi hannunka mai sanda a wata ganawa da ya yi dasu a kwanakin baya.
Tun farko wa'adin shugabanin na mulki ya cika amma gwamnati ta kara masu watanni shida har sau biyu kafin majalisar dokokin kasar ta amincewa shugaban kasa ya cigaba da kara masu lokaci har sai ya shirya sabon zaben kananan hukumomin kasar.
Lawali Adamu shugaban wata kungiya yace dokar tsawaita wa'adin shugabannin kananan hukumomi bata dace ba saboda yawancin kananan hukumomin suna da matsala. Abun da ya kamata a yi shi ne a tsayar da duk wani muna muna da cuku cuku a fada ma juna gaskiya.
Hamisu Hamidu shugaban kungiyar kulawa da rayuwa yace ba'a taru an zama daya ba. Ya kira gwamnatin Nijar ta cigaba da banbanta dan duma da dan kabewa tsakanin shugabannin kananan hukumomin Nijar. Duk wanda ya handami dukiyar jama'a a hukumtashi.
Alhaji Idi Abdu mai fashin baki akan harkokin yau da kullum yace bai kamata hukumcin da gwamnati ta dauka ya tsaaya kan shugabannin kananan hukumomi kawai ba. Yace babu yadda shugaban hukuma zai yi rub da ciki da dukiyar jama'a ba da sanin majalisar hukumarsa ba.
Ga rahoton Souley Barba da karin bayani.
Facebook Forum