Rundunar aiki da cikawa ta ‘yan sanda dake karkashin ofishin Babban Sufetan ‘yan sandan Najeriya ta cafke wasu kwamandoji hudu na ‘yan bindigar jihar Zamfara.
Kwamandojin da suka hada da Hamisu Sani, Shehu Sani, Yusuf Mande da Lawal Abubakar sun gayawa ‘yan sanda masu bincike cewa suna cikin kwamandojin ‘yan bindigar bangaren Buharin Daji.
Haka kuma zaratan ‘yan sandan dake karkashin jagorancin DCP Abba Kyari sun kuma cafke babban mai sayar da makamai ga ‘yan bindigar, wato Lawal Abubakar da yace akalla ya samar da Manyan bindigogi sama da dari ga ‘yan ta'addar.
Lawal Abubakar yace tun a baya dai marigayi Buharin daji ne ya neme shi da ya samo masa makamai inda a karon farko ya bashi Naira miliyan daya da dubu dari takwas, bayan kwana biyar Kuma Buharin dajin ya kara kiran sa ya bashi wasu Karin Naira miliyan daya da dubu dari takwas don kara samo masa wasu bindigogin inda yaje Barikin Ladi a jihar Filato ya samo su.
‘Yan bindigar sun ce suna daga cikin wadanda suka kokkona kauyuka da garuruwa da ma satar shanu da rakuma a sassan jihar ta Zamfara.
Mai magana da yawun Babban Sufeto na ‘yan sandan Najeriya, Bala Ibrahim ya shaidawa Muryar Amurka cewa dama jihar Zamfara ta dade tana fama da wannan matsalar ta ‘yan bindiga Kuma lallai wannan kamun zai kai ga bankado Karin wasu bayanai.
Masanin harkokin Tsaro, Mallam Kabiru Adamu yace aiki da fasahar zamani ya taimaka wajen tattara bayannan sirrin da ya kai ga cafke miyagun.
Tuni dai Zamfarawa suka barke da Murna bisa wannan Nasara da aka cimma ta kama kwamandojin ‘yan bindigar al'amarin da Ibrahim Janyau dake shugabantar kungiyar samar da zaman Lafiya a jihar Zamfara ke cewa hakan zai kwantar da Hankali a jihohin Zamfara, Sokoto, Kaduna da Katsina.
Ga karin bayani cikin sauti daga Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum