Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan-Ta'addar Boko Haram Sun Yi Ma Hauwa Liman Kisan Gilla


Hauwa Liman
Hauwa Liman

'Yan Kungiyar Ta'addar Boko Haram sun yi ma wata ma'aikaciyar lafiya mai aikin agaji kisan gilla a jihar Borno

Gwamnatin Najeriya, ta tabbatar da kisan wata mata ma’aikaciyar agaji da ‘yan kungiyar Boko Haram su ka kama a farkon wannan shekarar.

Ma’aikatar Yada Labarai ta Najeriya ta bayyana haka a jiya Litinin, inda ta ce an kashe Hauwa Mohammaed Liman, mai aiki a wani asibiti da ke samun tallafi daga kungiyar ba da agaji ta Red Cross.

Hauwa Liman, da Saifura Khorsa, wadanda ke ma kungiyar ICRC aiki, an kama su ne a watan Maris, lokacin da aka kai hari a wani asibiti da ke kauyen Rann a jahar Borno, tare kuma da Alice Loksha, wata jami’ar kiwon lafiya da ke aiki a asibitin da Majalisar Dinkin Duniya ta ke taimaka wa, karkashin shirin UNICEF.

‘Yan ta’addar ISIS ne tare da hadin gwiwar ‘yan Boko Haram su ka kama matan. Ma'ikatar Yada labaran ta kara da cewar gwamnati ta yi bakin kokarinta na ganin ta daidaita da ‘yan ta’addar don ceto rayuwar Hauwa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG