Za a yi wannan tattaunawa a birnin Jeddah,kwana daya a bayanda Tillerson ya sanar da cewar Amurka da Qatar sun sa hannu a yarjejeniyar da ta bukaci Doha ta dauki matakan shawo kan daukar nauyin ayyukan ta’addanci.
Ina nan a Qatar yau da irin himmar da shugaba Trump ya tafi Riyadh da ita a watan Mayu. Burin Amurka daya ne, a kawar da ayyukan ta’addanci daga doron kasa."
Sai dai kasashen Saudiya da Hadaddiyar Daular Larabawa, da Bahrain da kuma Misira sun fada a wata sanarwa cewa, yayinda suke yaba yunkurin Amurka na yaki da ta’addanci, yarjejeniyar da aka sawa hannu jiya Talata bata isa ba, kuma zasu ci gaba da sawa Qatar ido sosai wajen dakile daukar nauyin ayyukan ta’addanci.
Kasashen dai sun yanke huldar diplomasiya ne ranar biyar ga watan Yuni, suka dauki matakin rufe hanyoyin sufurin kasa da na sama da kuma na ruwa da Qatar. Kasashen da Saudiya ke jagoranta suna zargin Qatar da goyon bayan ayyukan ta’addanci, suka kuma ba Doha jerin sharuda goma sha uku da suke nema ta cika. Kasar Qatar tace a shirye take ta tattauna da nufin samun masalaha amma ba zata sadaukar da diyaucinta ba
Facebook Forum