Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tillerson ya Bar Qatar Ba Tare Da Cimma Wani Abin Kirki Ba


Sakataren harkokin wajen Amurka bai amsa tambayoyi ba game da ganawarsa da sarkin Qatar.

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya bar birnin Doha yau Alhamis bayan da ya gana da sarkin Qatar Sheikh Bin Hamad al-Thani, a wani sabon yunkurin diplomasiyya na baya-baya da ya dauka da zummar warware kiki-kakan da aka samu tsakanin Qatar da rukunin kasashen da suka hada da Saudiyya, da Hadaddiyar Daular Larabawa, da Bahrain, da kuma Masar.

Kungiyar kasashen da Saudi ke jagoranta dai sun zargi Qatar da goyon bayan akidar ta’addanci kuma sun ba Qatar jerin bukatu guda 13 bayan da suka yanke hulda da ita a farkon watan Yuni. Qatar dai ta ce a shirye take ta hau teburin neman sulhu amma ba zata taba sakin kimarta ta zaman kasa mai cikakken ‘yancin kanta ba.

Tun jiya Laraba Tillerson ya gana da ministoci daga kungiyar kasashen da Saudi ke jagoranat a Jeddah, amma bai yiwa ‘yan jarida bayani ba, bayan ganawar. Kafin ganawar, wani babban jami’i daga Hadaddiyar Daular Larabawa ya ce duk wata sasantawa da za ayi, ba zata tsaya kawai akan maganar kafofin samar da kudaden ta’addanci ba, dole ne a duba muhimman batutuwan da suka janyo rigimar.

Bayan wata ganawa da suka yi a makon nan da ministan harkokin wajen Qatar Mahammed bin Abdulrahaman al-Thani, Tillerson ya sanar da cewa Amurka da Qatar sun sanya hannu a kan wata yarjejeniya da ta tanadi cewa Qatar din zata dauki matakan da za su toshe duk wasu hannyoyin samar da kudaden gudanarda ayyukan ta’addanci.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG