Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majilisar Dinkin Duniya Ta Gano Wasu Kaburbura Har 38 A kasar Congo Wadanda Aka Binne Mutane Ba Bisa Kaida Ba


Gawarwaki dake rubewa a garin Damasak da aka kwato kwana kwanan nan, Maris 20, 2015.
Gawarwaki dake rubewa a garin Damasak da aka kwato kwana kwanan nan, Maris 20, 2015.

Majalisar Dinkin Duniya tace ta gano wasu manyan kaburbura 38 da aka bisa mutane a ciki a tsakiyar Congo inda rikici ya kashe dubban mutane tun daga Agustan bara. Wannan ne ya kai adadin manyan kaburburan da aka gano a yankin Kasai zuwa tamani, a cewar rundunar kwantar da tarzoma ta Majalisar Dinkin Duniya a Congo a jiya Laraba. Majalisa Dinikin Duniya ta kiyasta cewar mutane miliyon guda da dubu dari uku ne suka suka rasa muhallansu suna cikin gida sa’annan wasu dubu dari uku kuma suka arce zuwa makwabciya Angola tun barkewar rikicin a cikin watan Agusta. Kashe sarkin wata kalbila da yan sanda da sojoji suka yi shine ya tado da hare haren ramuwar gayya da wasu hare haren kuma tsakanin yan bindiga masu biyayya ga sarkin Kamuina Nsapu da dakarun tsaron gwamnati.

Wannan ne ya kai adadin manyan kaburburan da aka gano a yankin Kasai zuwa tamani, a cewar rundunar kwantar da tarzoma ta Majalisar Dinkin Duniya a Congo a jiya Laraba.

Majalisa Dinikin Duniya ta kiyasta cewar mutane miliyon guda da dubu dari uku ne suka suka rasa muhallansu suna cikin gida sa’annan wasu dubu dari uku kuma suka arce zuwa makwabciya Angola tun barkewar rikicin a cikin watan Agusta.

Kashe sarkin wata kalbila da yan sanda da sojoji suka yi shine ya tado da hare haren ramuwar gayya da wasu hare haren kuma tsakanin yan bindiga masu biyayya ga sarkin Kamuina Nsapu da dakarun tsaron gwamnati.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG