Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kalubalanci 'Yan Jarida Kan Labaran Da Suka Shafi Illolin Zuwa Cirani A Kasashen Ketare

Taron Ranar ‘Yan Jarida A Jamhuriyar Nijar
Taron Ranar ‘Yan Jarida A Jamhuriyar Nijar

Ranar ‘yancin aikin ‘yan jarida wani lokaci ne na bitar yanayin da ayyukan watsa labarai suka gudana a tsawon watanni 12 da suka shige.

Yau 3 ga watan Mayu ake shagulgulan ranar ‘yan jarida ta duniya, albarkacin zagayowar wannan rana a Nijar, Kungiyar ‘yan jarida mai kula da sha’anin tsaro da ci rani AJSEM Nijar da hukumar UNESCO sun shirya wani taro da nufin karfafa ayyukan fadakar da jama’a illolin cirani a lokacin fama da COVID-19.

Taron Ranar ‘Yan Jarida A Jamhuriyar Nijar
Taron Ranar ‘Yan Jarida A Jamhuriyar Nijar

Kungiyar ta ‘yan jarida mai kula da sha’anin tsaro da ci rani AJ-SEM Nigar da hukumar UNESCO sun shirya taron dake hada manema labarai da manajojin kamfanonin watsa labarai da nufin tattauna hanyoyin karfafa ayyukan fadakar da jama’a akan illolin cirani a wannan lokaci na fama da anobar COVID-19.

Ranar ‘yancin aikin ‘yan jarida wani lokaci ne na bitar yanayin da ayyukan watsa labarai suka gudana a tsawon watanni 12 da suka shige.

An tsara hakan ne domin duba hanyoyin kaucewa matsalolin da aka yi fama da su, dalili kenan da kungiyar AJ-SEM ta shirya wannan taro dake maida hankali akan matsalolin da suka shafi rayuwar ‘yan cirani da nufin jan hankulan kafafen yadada labarai da su karfafa shirye-shiryen fadakarwa a game da illolin cirani.

Taron Ranar ‘Yan Jarida A Jamhuriyar Nijar
Taron Ranar ‘Yan Jarida A Jamhuriyar Nijar

Taron wanda zai ci gaba da gudana har zuwa gobe Talata 4 ga watan Mayu, wata dama ce ta canza yawu a tsakanin masu zuwa fagen tattaro labarai da masu watsa shirye-shirye a kafafen sadarwa da kuma masu daukan dawainiyar wannan aiki abinda shugaban hukumar sadarwa ta CSC Dr. Kabirou Sani ke kallon shi a matsayin wani matakin nasarar cimma burin da aka sa gaba.

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da bunkasa sha’anin ilimi da kimiya da al’adu wato UNESCO da gwamnatin kasar Italiya ne ke daukan nauyin wannan sabon shiri na kungiyar AJ-SEM .

Taron Ranar ‘Yan Jarida A Jamhuriyar Nijar
Taron Ranar ‘Yan Jarida A Jamhuriyar Nijar

Da take jawabi a yayin bikin, wakiliyar hukumar kasar Italiya mai kula da ayyukan raya karkara a yankin Tafkin Chadi, Mme Muhameda Tulumovic, ta bayyana cewa ta hanyar bayar da labarai na zahiri a game da matsalolin cirani ne kawai za a iya katsewa ‘yan cirani hanzarin zuwa kasashen Yammaci ta barauniyar hanya.

A cewarta, wannan matakin zai iya taimakon ceto rayukan mutane da dama.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

An Kalubalanci 'Yan Jarida Kan Labaran Da Suka Shafi Illolin Zuwa Cirani A Kasashen Ketare
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

XS
SM
MD
LG