An kakkabo wani jirgin sama mai saukar Ungulu jiya, jirgin da yake dauke da wasu daga cikin ‘yan gwamnatin Islama ta Libya mai matsuguni a Tripoli
Ba bayanin ko mutane nawa ne a jirgin amma jami’ai sun ce ba sa sa ran akwai wanda ya tsira a cikinsu.
Masu ra’ayin Islamar sun zargi gwamnatin da suke adawa da ita da laifin harbo jirgin, wanda su kuma suka musanta wannan zargi.
Libya dai ta dare gida biyu tsakanin gwamnatin masu zafin kishin Islama da suka kwace ikon Tripoli da kuma gwamnatin da duniya ta amince da ita a kasar da suka tare a Tobruk.
Zuwa yanzu dai yunkurin Majalisar Dinkin Duniya na hada kan gwamnatocin ya faskara. Libya dai na fama da rikici da rashin daidaiton siyasa tun bayan hambarar da mulkin kama karyar Moammar Gadhafi da aka kashe a shekarar 2011.