Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Harin Ta'addanci Yankin Xinjiang A China


Mutane hudu ne suka mutu a wani al’amarin da wata kafar yada labarai ta gwamnatin China ta bayyana a matsayin “Harin Ta’addanci” da aka kai a Ofishin jam’iyyar Kwaminisanci dake Yammacin yankin Xinjiang mai yawan al'umma.

Jami’an yankin sunce mayakan hudu sun tada bamabama da aka hada a cikin gida jiya Laraba, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutum guda da kuma raunata mutane uku , bisa ga rahoton kafannin dillancin labarai na na gwamnati- Xinjhua . Rahoton yace, 'Yan sanda sun harbe maharan guda hudu , yayinda suka bayyana lamarin a matsayin harin ta’addanci.

An kashe daruruwan mutane a iyakar yankin Xinjiang a yan shekarun nan sakamakon mummunan tashin hankalin tsakanin musulman Uighur da kuma Yan kabilar Han na Sin, masu rinjaye.

Gwamnati ta dora alhakin tashin hankalin kan al'ummar Uighur masu tsatsa-tauran ra'ayi, wadanda ke neman yancin ci gashin kansu daga China. Sai dai kungiyoyin rajin kare hakin bil'adama da kuma Yan gudun hijira, suna masu ra'ayoyin cewa, Matsin lamba da kuma danniyar da gwamnati take yiwa addinin kailar Uighur da kuma al'adunsu ya haifar da tashin hankalin, zargin da gwamnatin China ta musanta.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG