Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Watanni Uku Da Kafa Dokar Ta Baci To ko Ina Aka Kwana?


Komandar rundunar Sojojin da aka tura yola domim dokar tabaci, Birgediya General Fatai Oladipo Alli kuma brigade komanda na tankokin yaki yayiwa Sojojin jawabi kafin turasu bakin aikinsu. Hoto Ibrahim Abdul'Aziz
Komandar rundunar Sojojin da aka tura yola domim dokar tabaci, Birgediya General Fatai Oladipo Alli kuma brigade komanda na tankokin yaki yayiwa Sojojin jawabi kafin turasu bakin aikinsu. Hoto Ibrahim Abdul'Aziz

Kimanin watanni uku ke nan da gwamnatin tarayya Najeriya ta kafa dokar ta baci a jihohi uku to ko ina aka kwana yanzu?

Kimanin watanni uku ke nan da gwamnatin Najeriya ta kakabawa johohin Adamawa da Borno da Yobe dukansu a arewa maso gabashin Najeriya dokar ta baci. To tun da aka kafa dokar ina aka kwana a jiha kamar Adamawa?

Kawo yanzu tun lokacin da aka kafa dokar ta baci a jihar Adamawa ba'a samu wani tashin hankali ba ko musayar wuta a jihar. Kwamandan rundunar tsaro ta jihar Birigediya Janaral Oladipo Fatayi Ali ya yabawa jihar da irin hadin kan da suke samu daga wurin al'umma.Ya ce abubuwa na tafiya daidai idan kuma aka cigaba hakan ba da dadewa ba abubuwa zasu daidaita. Ya kara da yabawa matakan da matasan jihar ke dauka.

Alhaji Abdullahi Bakari ya bayyana irin matakan da suke dauka domin tabbatar da zaman lafiya.Ya godewa matasa da bin umurnin da suka basu lamarin da ya sa babu wani matashi da ya karya doka ko ya bace.

Su kuma shugabannin addini sun godewa jama'a da suka bi hudubobin da aka yi a masallatai da mijami'u da basu bari an cima manufofin da suka sa aka kafa ma jihar dokar ta baci. Shi ma gwamnan jihar yabawa al'ummar ya yi domin sun taimaka manufar kafa dokar ba'a cimmata ba.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG