To amma wasu 'yan gudun hijiran da suka je garuruwansu a jihar da suka komo sun yi gargadin a yi taka tsantsan.
Ranar Talatar da ta gabata wasu 'yan siyasa dake zaune a Yola da Abuja suka sanar cewa zasu soma mayarda mutanensu garuruwansu musamman Michika da Madagali domin su gudanar da zabe. Saidai hukumar zabe tace shirin nasu bada yawunta ba ne.
Mr. Emmanuel Kwace daya daga cikin shugabannin yankin Michika ya bayyana nashi matsayin dangane da lamarin. Yace idan an shiga garin akwai tsoro domin babu kowa hatta dabbobi. Akwai kuma kabururuka da dan rami kawai aka tona aka saka gawarwaki ciki lamarin da ya sa suna ta yin wari. An zuba wasu gawarwaki cikin rijoyoyi abun da ya sa babu ma ruwan sha. Idan ba'a je an tsaftace garin ba babu yadda za'a iya zama a ciki.
Akwai wurare a Yola inda masu gudun hijira suka karbi katunan zabe. Suna iya su je can su yi zaben ba sai sun tafi garuruwan da aka kwato ba. Kamata yayi a dakata sai an gyara an tsaftacesu an yi tanadi kafin mutane su koma. Ban da haka 'yan Boko Haram na iya sake kai hari garuruwan da zara sun san sojoji sun janye kamar yadda suka yi a Gamboru da Gombi inda suka kashe mutane da dama.
Ga karin bayani.