Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Yi Amfani Da Kwarewar Larabci Wajen Yaki Da Akidar Ta’addanci A Najeriya - Asusun Koyar Da Larabci Na Najeriya

Taron Gasar Waka Da Larabci Da A Ka Gudanar A Abuja Bisa Tallafin Masarautar Shraja Ta Daular Larabawa.
Taron Gasar Waka Da Larabci Da A Ka Gudanar A Abuja Bisa Tallafin Masarautar Shraja Ta Daular Larabawa.

Asusun koyar da harshen Larabci na Najeriya ya yi alwashin amfani da gwanancewa a harshen wajen yaki da akidar ta’addanci a Najeriya da kasashen yankin Sahel.

Masana daga jami’o’i sun gabatar da jawabai a gagarumin taron gasar waka da Larabci da a ka gudanar a Abuja bisa tallafin masarautar Shraja ta Daular Larabawa.

“Ai cikar adon Musulmi na tabbata ne da kwarewa wajen iya magana da harshen Larabci kuma koyon harshen wata riba ce ta hulda da jama’a a sauran sassan duniya” In ji Farfesan Larabci na cibiyar Larabci ta Najeriya da ke Ngla Ibrahim Muhammad.

Taron Gasar Waka Da Larabci Da A Ka Gudanar A Abuja Bisa Tallafin Masarautar Shraja Ta Daular Larabawa.
Taron Gasar Waka Da Larabci Da A Ka Gudanar A Abuja Bisa Tallafin Masarautar Shraja Ta Daular Larabawa.

Farfesa Muhammad ya ce mafi gwanancewa a harshen Larabci a Najeriya mabiyin addinin kirista ne da hakan ke nuna harshen na kowa ne “sunan sa Farfesa Ishaq Ogunbiyi wanda a kan kasa duk lamuran Larabci da shi a duniyar Larabawa.”

Taron Gasar Waka Da Larabci Da A Ka Gudanar A Abuja Bisa Tallafin Masarautar Shraja Ta Daular Larabawa.
Taron Gasar Waka Da Larabci Da A Ka Gudanar A Abuja Bisa Tallafin Masarautar Shraja Ta Daular Larabawa.

Shugaban asusun Dr. Umar Adam Gusau ya ce ta hanyar harshen zai taimaka wajen fahimtar addini da zai kawar da gurguwar fassara da kan kawo masu kauce hanya da sunan addini.

Daga sashen Larabaci na jami’ar Abuja Farfesa Ndagi Muhammad ya ce za a koyi harshen da sauki in aka fara koyar da shi daga gida.

Mawaka masu magana da Larabci kamar ruwa irin Dr.Ibrahim Mu’azzam sun gabatar da baituka kan lamuran rayuwa.

Harshen Larabci ya dade a arewacin Najeriya don huldar kasuwanci tsakanin yankin da kasashen Larabawa na arewacin Afurka da kuma dalilin tafiya Makkah don aikin hajji.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG