Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An ji karar fashe fashe da harbe harben bindiga a birnin Kano


Kofar gidan da aka gano maboyar wasu 'yan Boko Haram a gundumar Mariri a Kano.
Kofar gidan da aka gano maboyar wasu 'yan Boko Haram a gundumar Mariri a Kano.

An ji karar harbe harben bindiga da asubahin yau Laraba a birnin Kano dake arewacin Najeriya

Shaidu sun bada rahoto cewa, an ji karar harbe harben bindiga da asubahin yau Laraba a birnin Kano dake arewacin Najeriya, inda mayakan kishin Islama suka kai kazaman hare hare da aka yi asarar rayuka cikin ‘yan watannin nan.

Mazauna yankin da manema labarai sun bayyana jin karar fashe fashe, daga nan suka ji karar harbe harben bindiga kafin sallar asuba a birnin da Musulmi suka fi rinjaye. Kawo yanzu babu rahoton wadanda abin ya shafa, yayinda jami’an tsaro suka ki cewa uffan dangane da lamarin.

Kano birni na biyu mafi girma a Najeriya, yana fama da tashe tashen hankali tunda ‘yan kungiyar kishin islaman nan mai tsats-tsauran ra’ayi Boko Haram ta kashe a kalla mtuane 185 a hare haren da ta kai watan jiya.

Hukumomi sun kafa dokar hana yawo daga karfe shida na dare zuwa shida da asuba.

Kungiyar Boko Haram tace tana neman a kafa shari’ar addinin Islama a duk fadin kasar inda Musulmi suke da rinjaye a arewaci yayinda Kirista suke da rinjaye a kudancin kasar. Sai dai wadansu masu sharhi kan lamura sun ce ana gani kamar tashin hankalin yana da alaka da rikicin siyasa.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG