Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'yan bindiga sun kashe yan sanda 3 a jihar Niger, Nigeria


Wasu jami'an 'yan sandan Nigeria
Wasu jami'an 'yan sandan Nigeria

Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba sun kashe yan sanda guda uku a jihar Niger da jikatta guda a lokacida suke kai hare hare guda biyu dabam dabam a unguwar M I Wushishi a birnin Minna da kuma garin Tungar Maje a karamar hukumar Suleija ta jihar Niger .

Wasu yan sanda guda biyu sun mutu, daya kuma ya jikatta a lokacinda wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba suka bude musu wuta. A daren Alhamis aka kai wannan hari a unguwar M I Wushishi dake Minna baban birnin jihar Niger.

Wakilin sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari ya aiko da rahoton cewa, al'amarin ya tayar da hankalin mazauna unguwar

Tunda farko, wasu yan bindiga suma da ba'a san ko suwane ba, sun kashe wani dan sanda mai mukamin kofur, a lokacinda suka kai hari wani ofishin 'yan sanda a garin Tungan Maje dake karamar hukumar Sukaija ta jihar Niger.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Niger, Mr. Richard Adamu ya tabbatar da harin kuma yace a halin da ake ciki ana gudanar da binciken dukkan hare haren guda biyu. Mr Adama ya shedawa wakilin sashen Hausa cewa, a harin da aka kai Tungan Maje yan bindigan sunyi awon gaba da bindigogi da kuma har sashe.

Aika Sharhinka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG