Jami'ai a arewacin Najeriya sun ce wasu matasa uku sun mutu yau jumma'a a lokacin da nakiyoyi suka tashi cikin wani gidan da ake harhada bam a asirce a garin Maiduguri mai fama da rashin kwanciyar hankali a yankin arewa maso gabashin kasar.
daya daga cikin kwamandojin rundunar hadin guiwa ta sojoji da 'yan sanda mai kula da tsaro a Maiduguri, Kanar Victor Oheneme, ya fadawa wakilin sashen Hausa Haruna Dauda cewa ba a san asalin ko su wanene wadannan matasan uku ba, ko ma 'yan wata kasa ce dabam, amma ana kyautata zaton cewa 'yan kungiyar nan ce ta Boko Haram.
Dakarun tsaro sun garzaya zuwa unguwar Kaleri dake bayangarin Maiduguri a bayan da aka ji karar tashe-tashen bam aka kuma ga wannan gidan ya rusa. Sun gano gawarwakin wadannan matasa tare da wasu bama-baman da aka harhada ba su tashi ba.
Hotunan da Muryar Amurka ta samu sun nuna yadda nakiyoyin suka rusa wannan gida har kasa. Bama-baman da ba su tashi ba, sun nuna cewa ana harhada wadannan bama-baman ne a cikin galan na man girki.
Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin hare-haren bam da harbe-harbe da dama a arewacin Najeriya, ciki har da mummunan harin da ya kashe mutane kusan dari biyu a Kano a cikin watan Janairu.