Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbi ‘Yan Sanda Biyu a Garin Ferguson


Shugaban rundunar 'yan sadan St. Louis Jon Belmar, ya nuna inda aka harbi daya daga cikin 'yan sandan
Shugaban rundunar 'yan sadan St. Louis Jon Belmar, ya nuna inda aka harbi daya daga cikin 'yan sandan

A garin Ferguson da ke kasar Amurka, an harbi 'yan sanda biyu yayin da ake wani bore.

‘Yan sanda a garin Ferguson na kokarin neman wanda ya harbi wasu jami’an tsaro biyu a Jihar Missouri da ke kasar Amurka.

Hakan ya faru ne yayin da masu bore su ka yi dandazo a bakin ofishin ‘yan sanda a garin na Ferguson bayan da shugaban rundunar Ferguson ya yi murabus.

A ranar larabar da ta gabata ne ma’aikatar shari’ar kasar Amurka ta fitar da wani rahoto da ke nuna cewa ana fifita fararen fatan garin Ferguson akan bakaken fata tare da cin zarafinsu.

“Abin da mu ka gano shi ne an yiwo harbi daga tsallakin titi kuma ya samu wasu ‘yan sandanmu biyu, kuma ga dukkan alamu su aka hara.” In ji shugaban rundunar ‘yan sandan yankin St. Louis, Jon Belmar.

Mr Belmar ya kara da cewa an harbi daya daga cikin ‘yan sandan ne a kafada yayin da dayan kuma aka harbe shi ne a fuska.

Sai dai ya kara da cewa a lokacin da aka garzaya da su wani asibiti da ke yankin suna cikin hayyacinsu.

Shugaban rundunar ‘yan sandan Ferguson, Thomas Jackson, ya yi murabus daga mukaminsa watanni bakwai bayan da wani dan sanda ya harbe wani bakar fata mai suna Michael Brown har lahira duk da cewa bayanai sun nuna cewa Brown ba ya dauke da makami.

XS
SM
MD
LG