A Rasha wata alkali Nataliya Mushnikova, ta fada jiya Lahadi cewa wani tsohon kwamandan 'Yansanda daga yankin Chechniya ya amsa cewa yana da hanu a kisan shugaban 'yan hamayya a kasar Boris Nemtsov, yayinda hukumomin kasar suke ci gaba da binciken wasu mutane hudu da ake zargi suna da hanu a wannan aika aikar.
Duka mutanen biyar sun bayyana a gaban wata kotu a Moscow jiya Lahadi. Ana ci gaba da tsaresu yayinda hukumomi suke gudanar da binciken kisan Nemtsov, sanannen dan adawa ga shugaba Putin ranar 27 ga watan jiya.
Ahalinda ake ciki kuma, 'Yansanda a India sun kama akalla mutane 22, bayan da gungun wasu suka farwa wani gidan yari suka kashe wani da ake zargi dan fyade ne a yankin da ake kira Nagaland, dake arewa maso gabashin kasar.
Har zuwa jiya lahadi ana ci gaba da zaman dar dar bayan da dubban mutane suka kai hari kan gidan fursinan a wurin da ake kira Dimapur suka fidda wani da ake zargi da laifin fyade suka lakada masa duka suka kashe shi sannan suka dauki gawarsa suka daura kan gofar babban agogon dake birnin.