Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

1965 Bakake Suka Samu 'Yancin Kada Kuri'a a Amurka


 Barack Obama shugaban Amurka
Barack Obama shugaban Amurka

Shugaban Amurka Barack Obama ya halarci bikin tunawa da gwagwarmayar neman 'yancin kada kuri'a da aka yi a Selma jihar Alabama

Jiya Lahadi dubban mutane suka hallara kan wata gada a garin Selma dake jihar Alabama a kudancin Amurka, domin su karrama da kuma zullumi kan sadaukar da gungun mutane kamarsu suka yi shekaru hamsin da suka wuce kan wannan gadar, a ranar da ta kasance kuma aka kira ta da "Lahadin da aka yi mummunar zub da jini".

Mutane masu yawa ne daga sassan Amurka daban daban suka ziyarci wanan wuri domin su halarci shirye shirye daban daban domin tunawa da waccar ranar.

Shekaru hamsin da suka wucen ranar 7 ga watan Maris a shekara ta 1965 'Yansanda suka doki mutanen tare da zuba musu borkonon tsohuwa a garin na Selma, lokcin da suka yi kokarin su yi maci daga Selma zuwa Montgomery, domin bayyana goyon bayansu kan baiwa duka jinsuna 'yancin kada kuri'a.

Mako biyu bayan aukuwar lamarin, shugaban yakin kare 'yancin Bil'Adama Martin Luther King, ya sami nasarar gudanar da macin daga Selma zuwa Montgomery. Zanga zangar ta taimaka aka zartas da dokar zabe ta 1965, dokar da ta haramta nuna banbanci saboda launin fatar mutum.

Atoni Janar na Amurka Eric Holder ya jijinawa 'yan gwagwarmayar na farko saboda jaruntakarsu wajen yakin ganin an kafa dokar. Yaci gaba da cewa "Ba tareda kakkautawa ba da sautin taku da suke yi, suka farkar da al'umar kasar, wajen ganin an yi adalci".

Tunda farko cikin jawabinsa na karrama wannan rana, shugaban Amurka Barack Obama yayi kira ga Amurkawa suyi aiki tare domin kara inganta kasar.

Shugaban na Amurkan, bakar fata na farko da zai jagoranceta, ya amince da cewa har zuwa yanzu da sauran rina-a-kaba, duk da haka ya gayawa dubban mutane da suka hallara ranar Asabar a Selma cewa, shi bai amince da masu cewa babu abunda ya sauya a kasar ba daga wancan lokaci.

XS
SM
MD
LG