Jiya Alhamis manyan hukumomin tsaron Amurka suka gargadi 'Yansanda da sauran jama'an tsaro cewa su sa ido kan yunkurin da kungiyar ISIS take yi na daukar 'yan ta'dda da zasu yi mata aiki ta amfani da internet.
Hukumar da take binciken manyan laifuffuka ta Amurka da ake kira FBI da kuma ma'aikatar tsaron gida ta Amurka sune suka bada wannan gargadi.
Wani jami'i ya gayawa kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa cewa "muna ci gaba da damuwa kan yadda kungiyar ISIS take janyo ra'ayin mutane su shiga kungiyar musamman ta wajen amfani da kafofin sadarwa, saboda haka muke kira ga al'uma su kasa kunne su sa ido kuma su tuntubi hukuma da zarar suka ga wani abu da suke shakkarsa.
Jaridar Washington Post ta buga labarin cewa hukumar FBI ta kama wani saurayi dan shekaru 17 da haifuwa a kauyen birnin Washington kan zargin ya taimakawa wani matashi ta wajen amfani da internet ya tafi Syria domin ya shiga kungiyar ISIS. Hukumar ta FBI bata bada karin bayani ba.
A lokacin da aka yi taron koli kan hanyoyin da za’a bi a yaki tsatsaucin ra'ayi cikin watan jiya a nan Washington, shugaba Barack Obama ya yi kira ga shugabannin kananan hukumomi su kara tuntuba da lura da matasa da basu da ayyukan yi. Irin wadan nan matasan ne masu tsatstsauran ra'ayi suke aunawa da kwadaita musu shiga kungiyotinsu.