Hukumomi sun ce an bindige wani mutum har lahira da daren jiya Asabar garin Portland na jahar Oregon, yayin da wata arangama ta barke tsakanin wasu magoya bayan Shugaba Donald Trump masu jeren gwanon motoci, da masu zanga-zanga kan wariyar da su ke zargin ‘yan sanda na wa bakaken fata, da aka fi sani da Black Lives Matter, a cewar ‘yan sanda.
Zuwa yanzu, bayanai na nuna cewa wanda aka harba din farar fata ne. Ba a tabbatar ko harbin na da nasaba, kai tsaye, da fadan da ya barke, bayan da masu zanga-zangar su ka tinkari tawagar motoci wajen 600, na magoya bayan Trump a tsakiyar birnin ba.
Kokarin ceto ran mutumin da aka harba.
Magoya bayan Trump sun yi ta taruwa a birnin, a ranakun Asabar na makwanni uku da su ka gabata. Masu zanga zangar sun yi yinkurin tsai da tawagar motocin, ta wajen tsayawa kan tituna da kuma katse gadoji.
Portland ya kasance fagen zanga-zanga da dare na tsawon watanni fiye da uku, tun bayan da ‘yan sanda su ka kashe George Floyd a Minneapolis. Gabanin wannan harbin, ‘yan sanda sun yi kame jiya Asabar su ka kuma shawarci mazauna wajejen su kauce ma maciyar birnin.
Facebook Forum