Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Sabuwa Game Da Zaben Amurka


biden trump 2020
biden trump 2020

Jami’an leken asirin Amurka sun daina yi wa majalisar dokoki bayani akan sha’anin tsaro ga zaben kasar, lamarin da ya janyo kakkausan martani daga ‘yan jam’iyyar adawa ta Demokrats.

Jami’an dakile ayukan leken asiri na Amurka sun ce ba za su sake yi wa majalisar dokoki bayani dangane da barazanar da ke tunkarar zaben shugaban kasa na watan Nuwamba mai zuwa ba, inda suka ce wannan bayanin da su ke yi na ido-da-ido, ya haifar da bayyanar wasu bayanan tsaro na sirri, da kuma sanya siyasa a bayanan.

Jami’an ofishin Daraktan hukumar leken asiri ta kasa sun fadawa wasu manyan ‘yan majalisar dokoki da kwamitocin majalisar wannan sauyin keke-da-keke a ranar Assabar, to amma sun ce duk da haka za’a samar da bayanan sirri akan barazanar da zaben na shugaban kasa na watan Nuwamba ke fuskanta, to amma ta wata hanyar daban.

Wani jami’in hukumar ta leken asiri ya fadawa Muryar Amurka cewa “mun daura damarar gudanar da ayukan mu kamar yadda doka ta tanada, kuma za mu tabbatar da sanar da majalisar dokoki akan komai cikin lokaci.”

Ya ci gaba da cewa “saboda inganci da tsare bayanan sirri masu muhimmanci daga fita da fadawa hannun da bai dace ba, za mu yi hakan ne ta hanyar ba da cikakku kuma kammalallun bayanai na sirri a rubuce. Abin da ya fi damun mu shi ne fitar muhimman bayanan sirri zuwa ga wadanda bai dace ba sakamakon irin ba da bayanan da ake yi a da.”

John Ratcliffe, Daraktan Hukumar Leken Asirin Amurka
John Ratcliffe, Daraktan Hukumar Leken Asirin Amurka

An kuma aikawa ‘yan majalisar dokokin wasiku da ke dauke da karin bayani akan sabon sauyin a ranar Assabar, daga Daraktan hukumar ta leken asiri, John Ratcliffe.

To amma kuma wasikar ta Ratcliffe ba ta bayyana takamaiman misali na abin da ya kira fitar bayanan sirrin ba, ko kuma yadda ake mayar da su siyasa sakamakon tsarin na baya na yi wa majalisar dokoki bayani ido-da-ido.

Sai dai kuma shugaba Donald Trump a ranar Assabar ta makon jiya, ya yi zargi ba tare da ba da hujja ba akan kwamitin majalisar wakilai na sha’anin tsaro da leken asiri da shugaban kwamitin Adam Schiff.

A shafinsa na twitter, Trump ya wallafa cewa “wata kila Schiff, da ma wasu, suna fitar da bayanan sirri domin yin labaran karya, labaran kanzon kurege irin na Rasha, Rasha, Rasha. Wannan lamarin na amfanarsu.”

To sai dai nan take shi ma Schiff ya maida martani da cewa “kamar yadda aka saba, Trump ya yi karya kuma yana ci gaba….. Trump ba ya son Amurkawa su san kokarin Rasha na taimakawa sake zabensa.”

Wannan sauyin da ya zo watanni 2 kafin zabe, ya haifar da kakkausan martani cikin gaggawa daga manyan ‘yan majalisar na jam’iyyar Democrats, wadanda suka zargi hukumar ta leken asiri da tozarta hakkin da ya rataya a wuyanta na ‘yan majalisar dokoki da kuma al’umma baki daya.

Haka shi ma babban dan Demokrats a majalisar dattawa Chuck Schumer, ya dora zargin sauyin akan Trump da gwamnatinsa, inda ya zarge su da kokarin yin rufa-rufa akan yunkurinsa na amfana daga katsalandan na kasashen waje.

Chuck Schumer, Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawan Amurka
Chuck Schumer, Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawan Amurka

A wata sanarwa Schumer ya ce “jami’anmu na leken asiri sun ce akwai wata barana yanzu haka da ke tunkarar tsarin dimokaradiyyarmu daga Rasha. Shugaba Trump na amfani ne kawai da John Ratcliffe domin boye gaskiyar lamarin ga Amurkawa – ma’ana shi ne wannan karon ma shugaban kasa na samun taimako na Kremlin.”

To sai dai kuma dan majalisar dattawa na Republican Marco Ruio, mukaddashin kwamitin majalisar dattawan na sha'anin tsaro da leken asiri, ya ce martanin ‘yan majalisar Democrats akan tarukan bayyana matsalolin da ke tunkarar zabe sun saba ka’ida.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG