WASHINGTON, D. C. - Sun bayyana a gaban kotun da alamun sun sha duka, kuma daya baya cikin hayyacinsa yayin sauraron karar.
Sanarwar da kotun ta fitar ta ce biyu daga cikin wadanda ake zargin sun amince da laifinsu a harin, ko da yake yanayin mutanen ya sanya ayar tambaya kan ko sun amince da laifinsu cikin walwala ne ko an tilasta musu. An yi ta samun rahotanni masu karo da juna a kafafen yada labaran Rasha wadanda suka ce uku ko duka mazajen hudu sun amince da aikata laifin.
Masu binciken sun tuhumi Dalerdzhon Mirzoyev mai shakaru 32; Saidakrami Rachabalizoda, 30; Shamsidin Fariduni, 25; da Mukhammadsobir Faizov, mai shekaru 19, da kai harin ta'addanci wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 130.
Laifin dai ya na dauke da girman hukuncin daurin rai da rai.
Kotun gundumar Basmanny ta birnin Moscow ta ba da umarnin cewa mutanen, wadanda dukkaninsu kafafen yada labarai sun bayyana cewa ‘yan kasar Tajikistan ne, a tsare su a gidan kaso har zuwa ranar 22 ga watan Mayu mai zuwa, yayin da za a cigaba da bincike.
Sauraron karar dai ya zo ne a daidai lokacin da kasar Rasha ta gudanar da zaman makoki a kasar saboda harin da aka kai a ranar Juma'a a wurin taron kade-kade na birnin Crocus da ya yi sanadin mutuwar mutanen akalla 137 da jikkata sama da 180.
Harin wanda wasu masu alaka da kungiyar IS ta dauki alhakin kai harin, shi ne mafi muni a kasar Rasha cikin shekaru da dama da suka gabata.
Hukumomin Rasha sun kame wadannan mutane hudu da ake zargi da kai harin ne tun ranar Asabar, tare kuma da tsare wasu mutane bakwai bisa zargin suna da hannu a harin, in ji Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a wani jawabi ga al'ummar kasar a daren Asabar.
Putin ya dai nemi daura alhakin harin akan Ukraine kuma ya yi ikirarin cewa an kama maharan a lokacin da suke neman tserewa can. Amma Kyiv ta musanta zargin.
-AP
Dandalin Mu Tattauna