WASHINGTON DC - A jiya Juma'a ne 'yan bindiga suka afkawa wani gidan rawa dake kusa da birnin Moscow, inda suka bude wuta tare da jefa abubuwa masu fashewa a harin ta'addancin mafi muni da aka taba kaiwa babban birnin Rasha a tsawon shekaru.
Tuni dai kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai harin.
A farkon watan da muke ciki ne, ofishin jakadancin Amurka dake Rasha yace yana nazarin rahotannin dake cewar masu tsattsauran ra'ayi nada shirin afkawa dandazon mutane a birnin Moscow, ciki harda gidajen rawa sa'annan ta gargadi Amurkawa su kaucewa irin wadannan wuraren.
Kakakin Majalisar Tsaron Amurka, Andrienne Watson yace gwamnatin Amurka tayi musayar wannan bayani da hukumomin rasha a bisa dacewa da dadaddiyar manufar nan ta "hakkin yin gargadi".
Saidai a jawabin daya gabatar a Talatar data gabata, Shugaba Putin yayi fatali da gargadin na Amurka a matsayin takalar fada inda yace matakin yayi kama da kokarin bata suna da yin barazana da haddasa rudani a tsakanin al'umma.
Za'a iya cewar Rasha ta taka rawa ta zahiri a yakin basasar kasar Syria, inda ta goyi bayan Shugaba Bashar al-Asad akan kungiyar ISIS.
A jiya Juma'a, sakamakon rahotanni kaiwa gidan rawa na "Crocus City Hall" ofishin jakadancin Amurka dake Moscow ya gargadi Amurkawa akan yin balaguro zuwa Rasha.
Dandalin Mu Tattauna