Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Taron Addu’o’in Neman Zaman Lafiya A Najeriya


Taron Malamai Na Addu’o’i A Najeriya
Taron Malamai Na Addu’o’i A Najeriya

Alamu na nuna cewa ‘yan Najeriya sun fara tunanin ba mafita ga matsalolin da suka dabaibaice kasar illa dukufa ga addu'a tare da komawa Ubangiji, tamkar dai yadda malamai suka yi ta kira a can baya.

Matsalar Boko Haram, satar mutane don neman kudin fansa, tayar da kayar baya don neman raba Najeriya, satar dabbobi da satar dalibai, sun taru sun jefa rayukan ‘yan Najeriya cikin halin kunci da zaman rashin tabbas, inda satar dalibai na baya-bayannan ma har yanzu iyaye da ‘yan uwan yaran na cikin jin radadin sa, kamar yadda daya daga cikin iyayen yaran makarantar Birnin Yauri ta jihar Kebbi ya fada.

Taron Malamai Na Addu’o’i A Najeriya
Taron Malamai Na Addu’o’i A Najeriya

Bisa ga lura da wadannan matsalolin ne da kuma ganin duk matakan da ake dauka sun kasa magance matsalolin ya sa malaman makarantun Islamiyya suka hadu don neman daukin ubangiji.

Shugaban majalisar koli akan lamurran addinin Musulunci a Najeriya, mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar wanda ya maganta ta bakin sarkin malaman Sakkwato Sheikh Yahaya na Malam Boyi ya ce ga irin yanayin da Najeriya take ciki yanzu ya zama wajiba a dukufa ga addu'o'in neman taimakon Allah.

Taron Malamai Na Addu’o’i A Najeriya
Taron Malamai Na Addu’o’i A Najeriya

Shugaban majalisar malaman makarantun Islamiyya, Malam Sidi A Sidi ya ce za'a ci gaba da addu'o'in a dukkan makarantun Islamiyya dake Sakkwato.

A jihar Kebbi ma gwamnatin jihar tare da fadar Masarautar Abdullahin Gwandu sun gudanar addu'o'in.

Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya shiga sahun malaman da suka gudanar da addu'o'in.

Taron Malamai Na Addu’o’i A Najeriya
Taron Malamai Na Addu’o’i A Najeriya

Sai dai kuma malamai na Jan hankalin jama'a akan cewa ko bayan addu'o'in akwai bukatar su kasance masu kyawawan halaye da kiyaye dokokin Ubangiji don samun taimakon sa.

Suarari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

An Gudanar Da Taron Addu’o’in Neman Zaman Lafiya A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00


XS
SM
MD
LG