Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan sanda Sun Musanta Harbin Wata Matashiya A Zanga-zangar Legas


'Yan sandan Najeriya yayin wani atisaye (Facebook/Rundunar 'yan sandan Najeriya)
'Yan sandan Najeriya yayin wani atisaye (Facebook/Rundunar 'yan sandan Najeriya)

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas da ke Kudu maso yammacin Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa wata matashiya ta mutu sanadiyyar harbin da suka yi don tarwatsa masu zanga-zangar kafa kasar Yarbawa.

Rahotanni da dama sun nuna cewa wata matashiya ‘yar shekara 14 da ke zaune a shago, ta gamu da ajalinta bayan da wani harsashin ‘yan sanda ya kauce hanya ya same ta.

Sai dai cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Olumuyiwa Adejobi, ya nesanta rundunarsu da mutuwar matashiyar.

“Rundunar ba ta harba ko da harsashi daya ba akan masu gangamin na Ojota a yau. An tsinci gawar ne lullube a wani waje da aka yasar da ita a bayan gidan man MRS a yankin Maryland, wajen nesa yake daga Ojota da ake gangamin, Mun ga bushesshen jini wanda hakan ya nuna ba sabuwar gawa ba ce.” Sanarwar ‘yan sandan ta ce kamar yadda gidan talabijijn na Channels ya ruwaito.

Masu zanga-zanga sun yi biris da gargadin jami’an tsaro suka gudanar da gangami a unguwar ta Ojota da ke birnin na Eko.

Dalilin shirya gangami wanda Sunday Igboho ya yi yekuwar a fito shi ne, neman kafa kasar Yarbawa inda jagororin taron suka ce cikin lumana za su gudanar da shi.

Amma hukukomin tsaron Legas sun haramta gangamin gudun kada bata-gari su yi amfani da shi su haifar da rudani.

Igboho shi ne mutumin da yake ikirarin jagorantar fafutukar, wanda yanzu haka jami’an tsaro ke nema ruwa a jallo bayan da suika samu bayanan sirri da ke nuna cewa yana tara makamai.

Hukumar tsaro ta DSS da ta kai samamen ta ce ta gano dumbin makamai da aka jibge a gidan tare da kama wasu hadimansa ciki har da mace guda.

Jami’an tsaron Najeriyar sun ce mutanen Igboho ne suka fara bude masu wuta, abin da ya sa suka mayar da martani har suka kashe biyu daga cikinsu. An jikkata jami’in tsaro daya a arangamar.

XS
SM
MD
LG