Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gargadi Shugabannin Sudan Ta Kudu Da Su Takawa Magoya Bayansu Birki


Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yana kira ga shugabannin Sudan ta kudu, kasar da yaki ya daidaita, su takawa magoya bayansu wadanda suke dauke da makamai birki.

Daga nan kwamitin yayi gargadin cewa ci gaba da kaiwa faren hula hari da cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya yana iya zama laifuffukan yaki.

Jakadan Japan Koro Bessho, wanda shine shugaban kwamitin sulhu na karba-karba mai wakilai 15, yayi magana a madadin kwamitin a birnin New York jiya lahadi,bayan da kwamitin yayi wani zaman gaggawa dangane da rikicin da yake gudana a Juba, babban birnin kasar. Ya kira hali da ake ciki a kasar a "zaman na gaggawa," yace an kashe akalla sojan kasar China daya wanda yake aikin kiyaye zaman lafiya, aka kuma jikkata sojojin Rwanda masu yawa a rangamar.


Zuwa yanzu babu kiyasin wadanda suka jikkata har zuwa daren jiya Lahadi, kuma har yanzu babu tabbas ko dakarun da suke biyayya shugaba Salva Kiir, da masu biyayya ga mataimakin shugaban kasa na farko Riek Machar zasu mutunta kiran da kwamitin sulhu yayi musu.


Wani gidan rediyo a Juba, ya bada rahoton mutane kusan metan da saba'in da shida ne aka kashe, yayinda wani kakakin Machar, yace akalla mutane 150 ne aka kashe, wadansu da dama kuma sun jikkata.


Duka shugabannin biyu sun bada sanarwa ta hadin guiwa suna kira ga jama'a su kai zuciya nesa, amma hakan bai cimma komi ba.

XS
SM
MD
LG