Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 9 Sun Mutu Wasu 8 Sun Jikkata a Ghana


Wasan da aka shirya din ya fara ne da misalign karfe 9 na daren jiya Laraba a agogon kasar, inda aka cika wani gidan wasa don yin wasannin sallah.

Kamar yadda aka saba a garuruwan Musulmi akan yi shagulgulan sallah, musamman ma kasashen Afirka. Haka ta faru a Zangon Kumasi ta kasar Ghana. Inda aka shirya wani wasan Sallah a wani wajen taron jama’a da ake kira Asawasi Community Center.

Wasu sun koka cewa wajen wasan ya cika sosai da daruruwan ‘yan kallo, to amma matsalar wajen kofar shiga day ace rak a filin. Bayan fara wasan ne sai wani ya kashe hasken wutar lantarkin wajen, har ta kai ga hakan ya firgita jama’a.

Daga nan ne sai mutane suka fara neman hanyar guduwa daga taron, a inda suka dinga turmutsutsun fita, wanda haka ya haddasa aka tattake wasu a kasa da yayi sanadiyyar mutuwarsu. Mutane tara ne suka mutu da suka hada da mata guda shida da maza guda uku. Sannan wasu guda takwas suka jikkata.

Abokin aikinmu Baba Yakubu Makeri ya yi hira da Kakakin ‘Yan Sanda na jihar Ashanti ASP Yusuf Tanko, inda ya tabbatar da labarin. Ya kuma ce suna nan suna binciken yadda abin ya faru. Bayan haka, abokin aikin namu ya tattauna da sarkin Zangon Kumasi Sultan Umar Faruk Sa’id.

Sai ya bayyan cewa wannan abin da ya faru, sun dade suna gargadin matasa da su guji shirya wasanni ire-iren wadannan da zasu iya wuce gona da iri. Ba don komai ba sai don tabbatar da an yi bukukuwan ranakun murna lami lafiya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG