Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Zambia Madugun Adawa Ya Amince Ya Goyi Bayan Shugaban Kasar Edgar Lungu


Edgar Lungu, shugaban Zambia
Edgar Lungu, shugaban Zambia

Shugaban ‘yan adawa na jamiyyar ZAMBIAN FOR EMPOWERMENT AND DEVELOPMENT PARTY (ZED) ya amince zai mara wa shugaba Edgar Lungu na jamiyyar Patriotic front baya, a zaben da za’a yi a ranar 11 ga watan Agusta na wannan shekarar.

A hirarsa da wannan gidan Radiyon Fred Mutesa yace Shugaba Lungu shine wanda yafi dacewa, kuma yake da basirar kara hada kan kasar tare da inganta rayuwar ‘yan Zambia.

Mutesa yace ba shugaba Lungu wannan goyon bayan ya biyo bayan binciken da ya gudanar cikin tsanaki ne,na wadanda zasu tsaya takarar shugabancin kasar wanda za ayi a cikin watan gobe.

Yace nayi imanin cewa shugaba Lungu shine wanda ya nuna alamun cika alkawari da kwarin gwiwa ga kasar mu, domin mutum ne mai kaifin basira da hangen nesa, hakan kuma ya fito fili a yawancin shawarwarin da ya yanke akan batutuwa da dama tun daga lokacin da ya kama shugabancin kasar a shekarar data gabata.

Mutesa yace misali shine zaban mataimakin shugaban kasa,babban mai shari'a na kasa, gwamnan babban bankin kasa, da kuma babban jami'in ‘yan sanda na kasa. Wanda wannan wata alama ce da nuna cewa shugaba Lungu mutum ne mai kaifin tunane.

XS
SM
MD
LG