Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Kira Ga 'Yan Sudan Ta Kudu Su Bar Kashe Junansu


Daga hagu, Machar ne, sai kuma Kiir
Daga hagu, Machar ne, sai kuma Kiir

Yayin da bangarori biyu da ke jayayya da juna a Sudan Ta Kudu ke cigaba da fafatawa, duk kuwa da jituwar aka cimma kwanan nan, Amurka ta yi kira ga bangarorin da su kai zuciya nesa.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka, jiya Asabar ta aika da sakon gaggauwa na kiran a kai zuciya nesa a Sudan Ta Kudu, bayan fada tsakanin bangarorin da ba su ga-maciji da juna a Juba, babban birnin kasar, ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 100 a jajabirin zagayowar ranar samun 'yancin kan kasar, karo na biyar.

Ma'aikatar Harkokin Wajen ta Amurka ta shawarci sojojin da ke biyayya ga Shugaba Salva Kiir da masu goyon bayan abokin jayayyarsa kuma Mataimakin Shugaban kasa na farko a yanzu Riek Machar, su kwance damara su daina fada.

An barke da luguden wuta da yammacin ranar Alhamis, bayan da wasu daga cikin sojojin da ke goyon bayan Shugaban kasar su biyar su ka rasa rayukansu a wata fafatawar da su ka yi da magoya bayan Machar a wani wurin duba ababen hawa daura da wani asibiti a birnin.

'Yan sa'o'i bayan nan, yayin da mutanen biyu ke ganawa a Fadar Shugaban kasar, masu saka ido na Majalisar Dinkin Duniya sun ba da rahoton mummunar musayar wuta daura da wani sansanin 'yan gudun hijira. Wasu shaidun ma sun ce musayar wutar ta ma zarce zuwa wasu sassan yankin.

Da Kiir da Machar, duk babu dayansu da ya iya bayyana musabbabin fadan na baya-bayan nan, to amma sun yi kira ga mabiyansu da su kai zuciya nesa.

Sabuwar kasar ta Afirka na kan murmurewa ne daga yakin basasa na tsawon shekaru biyu, wanda ke da nasaba da kabilanci, wanda aka fara tun a watan Disamban 2013 bayan da Kiir ya soke Machar daga matsayin Mataimakinsa. Yarjajjeniyar da aka cimma bara ta kawo karshen yakin, sannan wata yarjajjeniyar kuma da aka cimma a watan Afirilu ta kai ga kafa gwamnatin wuccin gadi ta hadin kan kasa da kuma sake maida Machar a matsayinsa na Mataimakin Shugaban kasa.

To saidai kuma Kiir, wanda dan kabilar Dinka ne, da Machar, wanda dan kabilar Nuer ne, har yanzu ba su cakuda sojojinsu zuwa runduna guda ba.

XS
SM
MD
LG