Shedu a Juba sun ce jiya Lahadi harbe harben ya watsu a bangarori da dama na birnin a musayar wutar da aka yi tsakanin ‘yan tawayen da jami’an tsaron gwamnati.
A baya dai ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi kira don tausasar ‘yan Sudan ta Kudun bayan wani kazamin fadan da aka tafka a ranar jajibirin bikin ranar ‘yancin kasar.
Inda takardar da Amurkan ta fita ta yi kira ga mayakan da ke marawa Shugaba Salva Kiir baya da kuma ‘yan tawayen da ke goyon bayan mataimakinsa na farko Riek Machar da su sasanta a tsakaninsu.
Hatta kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya sun yi alla-wadai da wannan rikicin da yaki ci ya ki cinyewa a birnin na Juba. Ciki har da hare-haren da aka kaiwa wasu jami’an diflomasiyya na Majalisar Dinkin Duniya a Juba a ranar Alhamis da ta gabata.