Kasar Somaliya na daya daga cikin kasashen da su ka fi samun yabo mafi kankanta a wannan rahoton da kungiyar ta yaki da almundahana ta fitar a yau dinnan Talata.
Mizanin rahoton ya bai wa kowace kasa maki tsakanin sifili zuwa 100. Baya ga kasar Somaliya, kasashen Afirka da su ka sami maki 20 ko kasa da haka sun hada da Sudan ta Arewa da Sudan ta Kudu da Guinea-Bissau, da Equatorial Guinea, da Chadi da kuma Iritrea.
Kasashen Afirka uku ne kadai su ka sami makin da ya dara 50- kuma su ne Botswana, da Cape Verde, da kuma Rwanda.
Kungiyar ta Transparency International ta ce Afirka ta dan cigaba a ma’aunin habbakar dan adam da kuma tattalin arziki. To amma wannan kungiyar mai hedikwata a Berlin ta ce an ga tabarbarewar gaske ta fuskar kare lafiyar jama’a da batun bin doka da oda.