Shugabannin kasashen Afirka kusan 30 suke halartar bukukuwan da ake yi, inda a yau din suka yi ta gabatar da jawabai kan yadda za a iya samun wanzuwar zaman lafiya da kare hakkin al'umma.
A shekarar 1914, turawan mulkin mallaka na Ingila suka hada yankuna uku da sukewa mulkin mallaka dabam-dabam a lokacin, suka zamo kasa guda da suka sanya ma suna Najeriya. Yankunan sune Lardin Arewa, Lardin Kudu da kuma Lardin Lagos.
Wakilinmu Umar Faruk Musa ya aiko da cikakken bayani daga Abuja.