Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Tarwatsa Zanga-Zangar Lumana a Abuja


Mata masu zanga-zanga a Abuja kafin 'yan sanda su tarwatsa su.
Mata masu zanga-zanga a Abuja kafin 'yan sanda su tarwatsa su.

Wasu matasa sun nemi yin zang-zangar nuna rashin jin dadin kashe-kashe a arewa maso gabashin Najeriya, amma 'yan sanda suka kore su.

Kungiyoyin Matasa daga sassa daban daban na Najeriya sun yi wani gangami na nuna bacin ransu game da yawan kashe kashen rayuka da kuma rashin tsaro da ke cigaba da yin kamari a arewacin najeriya, musamman a jihohin dake arewa maso gabas.

Shekaranjiyan nan aka kashe dalibai masu yawan gaske a Makarantar Gwamnatin Tarrayya dake Yadin Buni a Jihar Yobe, a wani harin da 'yan bindigar da ba a tabbatar da ko su wanene ba suka kai.

Wakiliyarmu, Medina Dauda, wadda ita ma aka ji mata rauni a lokacin da ake kai farmaki kan masu zanga-zangar, ta aiko mana da cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG