Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dage Haramcin Saye Da Rijistar Sabon Layin Wayar Salula A Najeriya


Isa Ali Pantami
Isa Ali Pantami

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dage haramcin saya da yin rijistar sabon layin wayar salula wato SIMCARD a turance.

Hakan na nufin a yanzu ‘yan kasar na da damar samun sabon layin wayar salula, tare da yin rijista da lambar shaidar zama dan kasa wato NIN.

Ministan sadarwa da tattalin arzikin fasahar zamani, Dakta Isa Ali Pantami ne ya bayyana hakan bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fannin sadarwa inda suka cimma wannan matsaya bayan nazari mai zurfi, tare da yin gyara ga kudurin shaidar dan kasa domin ba da damar yin rijistar layin waya.

Dakta Pantami ya ce wannan matsaya na nufin cewa, gwamnati ta dage haramcin sayen sabon layi da ta yi a cikin watan Disamban shekarar 2020, kuma ‘yan kasa za su iya fara saye da yin rijistar layuka daga cikin watan nan na Afrilu da mu ke ciki.

Ministan ya kuma bai wa hukumar sadarwa ta Najeriya wato NCC, da hukumar da ke ba da katin shaidar zama dan kasa wato NIMC, umarnin tabbatar da cewa, duk kamfanonin sadarwa da ‘yan kasa sun bi tsarin kudurin shaidar dan kasa a duk lokacin sayar da sabon layi da kuma yin rijistarsa.

Karin bayani akan: Isa Pantami​, NIN, NCC, Boko Haram​, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Hakan dai na nufin cewa, za'a fara aikin aiwatar da wannan sabon tsari da samun sabbin layukan wayar tarho gadan-gadan a rana daya da zarar an gama aikin tantancewa, kuma an bi duk dokokin da aka tsara.

A cikin wata sanarwa, mai taimakawa minista Pantami a fannin aikin fasahar bayanai, Dakta Femi Adeluyi, ya ce masu ruwa da tsaki sun amince da wannan kuduri ne a ranar 4 ga watan Febrairun shekarar 2020, a yayin da aka yi gyara a kudurin a cikin watan Maris na shekarar 2021 da muke ciki, kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da fara aikin aiwatarwa a radar 21 ga watan Maris na shekarar 2021.

According to the statement, the final amendments to the revised policy, based on the directives of Buhari to make the use of National Identification Number (NIN) mandatory for all SIM registration, were completed on April, 14, 2021.

Sanarwar ta kara da cewa, an yiwa kudurin gyare-gyaren karshe ne bisa umarnin da shugaba buhari ya bayar na yin amfani da lambar shaidar zama dan kasa wato NIN ta zama tilas ga duk rajistar layin waya, wanda aka kamalla gyare-gyaren a ranar 14 ga watan Afrilu da mu ke ciki.

XS
SM
MD
LG