Ministan sadarwa na Najeriya Ali Isa Pantami ya mayar da martani ga kafafen yada labaran da suka wallafa rahoton cewa Amurka ta saka sunansa a jerin ‘yan ta’adda.
‘Yan Najeriya sun wayi garin a ranar Litinin da rahotanni a kafafen yada labarai na yanar gizo, wadanda suka ba wallafa cewa Amurka ta saka Pantami cikin jerin sunayen ‘yan ta’adda.
Sai dai cikin martanin da mayar a shafinsa Twitter @DrIsaPantami, ministan ya ce, kotu ce kadai za ta raba su da dukkan kafafen yada labaran da suka wallafa wannan labari.
“Duk manyan kafafen yada labaran da suka bata min suna, za su hadu da lauyoyina a kotu.” Pantami ya ce.
Karin bayani akan: Isa Pantami, Boko Haram, Nigeria, da Najeriya.
Ko da yake, kafar yada labarai ta NewsWireNGR wacce tana daya daga cikin wadanda suka wallafa labarin, ta ce ta janye rahotonta, amma Pantami ya ce, ta makara.
“@NewsWireNGR, na lura da janye labarin da kuka yi daga binciken da kuka gudanar, amma ka’idar bincike da aikin jarida ya tanada, ya bukaci a yi binciken ne kafin wallafa labarin, ba bayan haka ba.” In ji Pantami
Kafafen yada labaran da suka wallafa rahoton cewa ministan ya shiga jerin sunayen ‘yan ta’adda, sun ruwaito cewa Pantami ya nada alaka ta kut-da-kut da wasu manyan shugabannin kungiyar Boko Haram, zargin da ministan ya musanta.
“Lakcocina da na kwashe shekara 15 ina sukar masu yada munanan akidoji sunan nan, ciki har da mukabaloli da na yi, wadanda suka saka rayuwata cikin hadari. Idan mutum ba ya jin Hausa, ya nemi tafinta adili mai jin Hausa, ya fassara masa abin da na fada.” Pantami ya fada a shafinsa na Twitter.
A bata day kungiyar ta Boko Haram ta taba barazanar hallaka ministan saboda kallon da suke masa na malamin addini da ya shiga harkar gwamnati.
Ministan ya kara da cewa, dangane da batun matakin da gwamnati ta dauka na yin rijistar layin waya da ta shaidar dan kasa – wato NIN-SIM don magance matsalar tsaro, “ba gudu, ba ja da baya.”
Daga cikin jaridun da suka wallafa labarin akwai Daily Post, NewsWireNGR, Daily Independent da dai sauransu. Tuni NewsWireNGR ta ce ta janye nata labarin.