Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Karbi Fam Miliyan 4.2 Na Kudaden Da Aka Kwato Daga Hannun Ibori


Abubakar Malami
Abubakar Malami

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta karbi fam miliyan 4.2 da aka kwato daga hannun dangin tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori, wanda ya wawure kudaden al’uma kamar yadda kakakin Atoni Janar din kasar Umar Jibrilu Gwandu ya tabbatarwa da Muryar Amurka.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin ministan shari’a kuma antoni janar na tarayyar Najeriya, Abubakar Malami ya fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta tabbatar da lamarin cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya ta karbi fam miliyan 4.2 da doriya wadanda aka kwato daga ‘yan uwan tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori da ya wawure a lokacin da yake kan karagar mulki.

An ruwaito Abubakar Malami, na cewa, wannan wannan ci gaban ya nuna irin martabar da Najeriya ta samu ta hanyar bayanan yadda aka kwato wasu kudadde da aka sata daga Najeriya a madadin yin amfani da su wajen aiwatar da ayyukan da suka shafi jama'a.

Idan ba a manta ba a ranar 3 ga watan Mayun ne ministan shari’a, Abubakar Malami, ya sanar da cewa, kasar Burtaniyya za ta dawo wa da Najeriya wasu kudadde da ‘yan kasar suka sace nan ba da jimawa ba lamarin da ya tabbata a ranar 18 ga watan Mayun da mu ke ciki.

Malami dai ya yi bayanin cewa, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, na aiki tukuru don tabbatar da dawo da kudadde da kadarorin kasar da aka wawure aka ajiye a kasashen waje.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG