Jami'an tsaro musamman 'yan sanda suna samun kalubale a harkokin tsaro domin mutane da yawa suna da makamai a hannunsu. Kananan makamai suna yaduwa a hannun mutane ba bisa kaida ba. Hakan sai kara haddasa miyagun laifuka ya keyi.
A wata tattaunawa da kwamishanan 'yan sandan jihar Amanbra kudu maso gabashin Najeriya Usman A Gwari yace abubuwan da suka fi damun rundunar su su ne garkuwa da mutane da kuma fashi da makami. Wadannan laifukan su ne suka fi addabar jihar kuma duka da makamai ake aikatasu. Amma kwanan nan suka kama wasu masu manya manyan laifuka ciki har da mai sayar da bindigogi ma 'yan fashi da garkuwa da mutane. An samu mutumin da bindigogi iri-iri. Haka kuma rundunar ta kama wata mata mai bada hayar makamai da motoci da bata gari ke yin anfani da su wurin yin fashi da garkuwa da mutane.
A can Rivers kuma rundunar 'yan sandan jihar ta kama wani jerin gwanon motoci da ke raka wata gawa amma bayan samun bayanan siri jami'an tsaro sun binciki motar da ake zaton gawa ce a ciki amma mai makon gawar dimbin makamai aka gano. Mr Tunde Ogunshakin kwamishanan rundunar 'yan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin. Yanzu rundunar tana tsare da mutane biyar. Ana tuhumarsu da aikata wannan danyan aikin.
Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto.