Idan ba'a manta ba yarinyar mai suna Aisha Rabiu ta yi kusan makonni uku kwance a asibiti a sume bata iya magana ko ma bude idanunta a wani asibiti a Kontagora garin da aka yi mata fyade. Muryar Amurka ta bi sawun lamarin tun lokacin da ya faru har sai da gwamnatin jihar ta kai yarinyar asibitin IBB dake Minna inda ta farfado har ma aka sallameta.
Yayin da wakilin Muryar Amurka Mustapha Nasiru Batsari ya samu ya zanta da matasan daya daga cikinsu ya bayyana yadda suka sa kwaya cikin kunun da suka bata da yadda shi yayi anfani da yarinyar. Yace bayan hakan sai bata iya tashi ba.
To yanzu an fara shari'ar inda aka gabatar da matasan su biyu dukansu 'yan shekaru goma sha takwas a gaban kotu a garin Kontagora da tuhumar baiwa yarinya 'yar shekara 14 kwayar maye kana suka yi mata fyade. Lauyan gwamnati Abubakar Suleiman yace suna tuhumar Ahmad Zakari da baiwa yarinyar kwayar bugarwa da kuma yi mata fyade. Suna kuma tuhumar dayan Rufai Umar da taimakawa ta hanyar bayar da daki domin yin barnar al'amarin da ya sabawa doka.
To amma a nasu gefen matasan sun shaidawa alkalin cewa basu san da wanna batun ba saboda haka sun ki su amsa laifinsu. Kan haka ne lauyan gwamnati ya nemi kotu ta basu daman su kawo shaidunsu. Mai shari'a ya amince da bukatar lauyan gwamnati yayin da ya daga karar amma babu ranar komawa kotun sabili da rashin kasancewar lauyan dake kare wadanda ake tuhuma a kotun.
Lauyan gwamnati Abubakar Suleiman yace zasu gabatar da sheidunsu domin duniya ta sani cewa abun da suke tuhumar matasan da yi lallai sun aikata. Badan lauyan matasan baya kotu ba da ko wanshekare zasu iya komawa kotun. Lauyan da ya je kotun a madadin kungiyar lauyoyi mata ya yi bayani kan maganar. Yace burinsu shi ne a yi adalci a shari'ar. Wadanda suka aikata laifin a yi masu hukunci kwatankwacin lafin da suka aikata. Ita ma yarinyar da aka yiwa fyade a biyata diya kwatankwacin abun da a ka yi mata.
Ga karin bayani.