Yayin da gwamnan jihar Dr. Babangida Aliyu ke kaddamar da wani sabon asibiti da hanya, yace gwamnatinsa ta cika duk alkawuran da tayi lokacin neman zabe. To sai dai 'yan adawa basu yadda da hakan ba.
Alhaji Umar Sha'aibu, dan kwamitin zartaswa a jam'iyyar APC a jihar ta Neja, yace "hanyar da gwamnan yaje kaddamarwa tsawonta kilomita 150 amma kilomita 50 kawai aka yi. Har yanzu hanyar na nan ba'a kammalata ba. Gwamnan yayi alkawarin gina hanya mai tsawon kilimita goma goma a kowace karamar hukuma su 25 amma bayan shekara bakwai kan mulki ba'a yi komi ba. Amma kuma ana cirewa kowace karamar hukuma kudi."
Alhaji Sha'aibu ya kara da cewa "akwai batun gina otel mai daraja ta biyar da aka ce za'a kashe kudi nera biliyan biyar amma ko filin ma ba'a gyara shi ba balantana a soma gini. An kuma kashe kudi a kan otel din."
Saidai gwamnatin jihar tace kalamai ne kawai na 'yan adawa. Danladi Ndayabo daraktan yada labarai na gwamnan yace babu ko shakka sun taka rawar gani. Yace duk alkawuran da suka yi sun cika a wasu wurare ma sun wuce alkawarin.
Ga rahoton Nasiru Mustapha Batsari.