Amurka ta kara kaimin matsawa Pakistan lamba da nufin ganin an saki wani jami’in diplomasiyanta da ake zargi da harbin bindiga da ya yi sanadin mutuwar ‘yan kasar Pakistan uku.
Jami’an kasar Amurka sun bayyana jiya Talata cewa, gwamnatin shugaba Obama tana kayyade irin huldar siyasa da take yi da Pakistan, sai dai kawo yanzu, tattaunawar da ake shirin yi ranar 24 ga wannan wata na Fabrairu tsakanin manyan jami’an Amurka da na Afghanistan da kuma Pakistan yana nan kamar yadda aka tsara.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka P.J Crowley ya shaidawa Muriyar Amurka cewa, an takaita batutuwan da ake tattaunawa tsakanin manyan jami’an Amurka da kuma na Pakistan. An yi harbin ne ranar 27 ga watan janairu a arewa maso gabashin birnin Lahore.
Jami’an diplomasiyan Amurka sun ce jami’in da hukumomin kasar Pakistan suka bayyana mai suna Raymond Davis, ya harbe ya kuma kashe wadansu ‘yan kasar Pakistan biyu domin kare kanshi yayin wani yunkurin yi mashi fashi. An kashe mutum na uku lokacin da motar ofishin jakadancin ta banke shi a kan hanyarta zuwa inda aka yi harbin.