Kwararru a Bankin Duniya suna hasashen za’a fuskanci rashin tabbas kan farashin kayan abinci,san nan farashi dangin hatsi ko tsaba zai haura daga yanzu zuwa 2015.
Farashin wasu kayan bainci sun kusa, koma sun haura farashi da suka kai a 2008,lokacinda tsadar abinci ta janyo mumunar zanga zanga a wasu kasashe.
Shugaban Bankin Duniyan Robert Zoellick, yace tashin farashin abinci shine babban kalubale dake fuskantar galibin kasashen dake tasowa.A kasashe matalauta,mutane suna kashe rabin samunsu kan abinci,saboda haka idan aka sami tashin farashi hakan yana janyo wahala sosai.
Kwararru daga bankin sunce sai tayu akwai mutane kamar milyan dubu daya dake fama yunwa a fadin Duniya baki daya ahalin yanzu.Tsadar abinci zata iya tilastawa talakawa su gwammace neman abinci mai makon jinya da neman ilmi.
Sharhin ya biyi bayan rahotanni dake cewa matsalar yanayai daaka samu a wasu sassa dake noma a bainci ya kara farashin alkama,shinkafa,hatsi,sukari da wasu kayan amfanin gona.