Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yarjejeniyar Kayyade Makaman Nukiliya Ta Fara Aiki

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton da takwarn aikinta na Rasha,Sergei Lavrov,a bikin tabbatar da yarjejeniyar.
Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton da takwarn aikinta na Rasha,Sergei Lavrov,a bikin tabbatar da yarjejeniyar.

Jiya Asabar ce sabuwar yarjejeniyar kayyade makaman Nukiliya da Amurka da Rasha suka kulla ta fara aiki.

Jiya Asabar ce sabuwar yarjejeniyar kayyade makaman Nukiliya da Amurka da Rasha suka kulla ta fara aiki.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton da takwaran aikinta na Rasha Sergei Lavrov suka yi musayar kasidu da hukumance suka tabbatar da ayyana wan nan nan yarjejeniya.Sun yi haka ne a gefe guda a taronda ake yi kan harkokin tsaro a birnin Munich na kasar Jamus.

Sabuwar yarjejeniyar wacce zata yi aiki na shekaru 10,zata rage yawan makaman Nukiliya da Amurka da Rasha zasu mallaka,ko wace kasa zata rike makaman dubu 1,550,daga 2,200 da ko wacce take dashi ahalinyanzu.

Karkashin wan nan yarjejeniya kowani bangare sai shaidawa daya bangaren bayanai kan adadin makamanta,wadanne iri ne kamar yadda yake cikin yarjejeniyar da kuma inda aka adanasu,cikin kwanaki 45.

XS
SM
MD
LG